Zan fasa ƙwai kowa ya ji - Warner

Hakkin mallakar hoto warner tv
Image caption Warner yana daga cikin jami'an Fifa da ake zargi da cin hanci da rashawa

Tshohon mataimakin shugaban hukumar Fifa Jack Warner ya ce zai fayyace dukkan abubuwan da ya sani kan cin hanci da rashawa a hukumar ta kwallon kafa ta duniya.

Warner wanda ya ce yana jin tsoron kada a hallaka shi ya fadi haka ne a wata kafar yada labarai a lokacin da aka yi hira da shi.

Ya kuma ce zai iya alakanta jami'an Fifa da babban zaben da aka yi a kasarsa Trinidad and Tobago a shekarar 2010.

Warner yana daya daga cikin mutane 14 da Amurka ta zarga da cin hanci da rashawa a hukumar Fifa.

Wani tsohon jami'in Fifa kuma daya daga cikin masu bayar da shaida Chuck Blazer ya ce sun karbi cin hanci da rashawa a hukumar.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ce ta zarge su da karbar cin hanci da yankan baya da aka kiyasta ya kai ta sama da dala miliyan 150 a cikin shekaru 24.