Milner ya sasanta da Liverpool

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Milner zai koma Anfield

Liverpool ta amince ta kulla yarjejeniya domin sayen dan kwallon Ingila James Milner daga Manchester City.

Dan shekaru 29, zai bar Etihad idan kwangilarsa ta kare a ranar daya ga watan Yuli kuma idan har aka gwada lafiyarsa a Anfield.

Milner ya lashe kofunan gasar Premier biyu, da na FA daya da kuma na League cikin shekaru biyar a Man City.

Ya buga wa Ingila, wasanni sau 53 sannan ya zura kwallaye takwas a kakar wasan da ta wuce.

Milner ya koma City ne daga Aston Villa a shekara ta 2010 inda aka siye shi a kan fan miliyan 26 a lokacin Roberto Mancini.