Za a binciki cin hanci a Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Afirka ta Kudu ce ta fara karbar bakuncin kofin duniya a Afirka

Jami'an tsaron Afirka ta Kudu za su gudanar da kwarya-kwaryan bincike kan mahukuntan da su ka bayar da cin hanci domin a bai wa kasar damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2010.

Sanarwar ta fito ne bayan da wata jam'iyar adawa ta mika takardun bayanai ga mahukunta da ake zargin bayar da cin hanci da rashawa ga jami'an Fifa.

Tsohon jami'in Fifa Chucks Blazer ya bayyana cewar sun karbi cin hanci da rashawa da suka jibanci karbar bakuncin kofin duniya a shekarar 1998 da kuma 2010.

Mahukuntan kasar Afirka ta Kudu sun karyata zargin cewar sun bai wa mahukuntan Fifa cin hanci.

An tuhumi Afirka ta Kudu da bayar da cin hancin kudi dala miliyan 10 ga jami'an Fifa wadan da suka zabi Afirka ta Kudu maimakon Morocco wacce suka yi takara tare.