Wasika ta nuna yadda aka biya Fifa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Afrika ta Kudu ta ce ba ta bayar da cin hanci ba ga Fifa

Wata wasika da ake ganin shugaban hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu, Danny Jordan ne ya rubuta, ga alamu ta kara fito da zarge-zargen cuwa-cuwa a Fifa.

A cikin wasikar cewa gwamnatin Afrika ta Kudu ta yi duk abin da za ta iya domin boye wasu kudade da ta tura na miliyoyin daloli ga Fifa.

Wasikar wacce ake tseguntawa wata jarida, an rubutane shekaru 8 da suka gabata, zuwa ga sakatare janar na Fifa, Jerome Valcke.

Wakikar ta na kuma nuni da cewa bayan wata tattaunawa tare da ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu, Mr Jordan ya nemi a tura kudaden ta wasu hanyoyi da bana kai tsaye ba.

Jami'an Afirka ta Kudu sun hakikance cewa babu cin hancin da aka biya saboda karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar duniyar a shekarar 2010.