Henderson na bukatar Sterling a Liverpool

Image caption Tun a baya Sterling ya ce ya na fatan ya dunga daukar kofuna a gaba

Jordan Henderson na fatan Raheem Sterling zai kawo karshen takaddamarsa da Liverrpool, sannan ya ci gaba da murza leda a kakar wasannin badi a Anfield.

Sterling ya ki amincewa ya tsawaita kwantiraginsa da Liverpool, amma Brendan Rodgers ya ce ya na fatan dan kwallon zai kammala yarjejeniyar shekaru biyu da suka rage masa a Anfield din.

Henderson wanda zai yi wasa da Sterling a wasan sada zumunta da Ingila za ta yi ranar Lahadi, ya yi watsi da yadda ake sukar dan kwallon.

Sabon kociyan Real Madrid Rafael Benitez ya ce suna sha'awar Sterling, wanda ake rade-radin zai koma murza leda a Manchester City a badi.

Sterling ya jawo kace nace a lokacin da ya ki amincewa da tayin fan 100,000 a duk mako da Liverpool ta ce za ta dunga biyansa, kuma eja dinsa Aidy Ward ya ce ko fan 900,000 za a bashi ba zai rattaba kwantiragin ba.