Liverpool ta rage kudin kallon wasanninta

magoya bayan kungiyoyin Premier sun yi ta kiraye-kirayen da a rage kudin kallon wasanni

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

magoya bayan kungiyoyin Premier sun yi ta kiraye-kirayen da a rage kudin kallon wasanni

Kungiyar Liverpool ta sanar da rage kudaden dukkanin tikitin shiga kallon wasanninta a kakar 2015-16.

Liverpool ta cimma wannan matsayar ne bayan da ta yi aiki kafada da kafada da rukunan kungiyoyin da suka kunshi magoya bayan kungiyar.

Wani bincike da BBC ta gudanar ta gano cewar karamin benan kallon tamaula a Anfield ya kai fan 37, idan aka kwatanta da na sauran kungiyoyin Premier da matsakaicni farashin su yake sama da fan 28.

Shugaban kwamitin magoya bayan Liverpool Bob Humphries ya ce sun ji dadi da wannan ragin da kungiyar ta yi, kuma haka ya nuna cewa an saurari kukun da suka dunga yi a baya.

Wasu magoya bayan Liverpool sun yi zanga-zanga kan tsadar tikitin kallon wasannia a Anfield a karawar da ta yi da Hull City a watan Oktoba.

A watan Afirilu kuwa magoya bayan Liverpool din sun kauracewa karawa ta biyu da kungiyar ta yi da Hull City din, bisa tsadar tikiti da ya kai fan 50.