Tennis: Wawrinka ya doke Tsonga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wawrinka na fatan lashe gasar Roland Garros karo na biyu

Stan Wawrinka ya yi waje da Jo-Wilfried Tsonga a gasar kwallon tennis ta French Open a wasan daf da karshe da suka yi ranar Juma'a.

Wawrinka ya doke Jo-Wilfried Tsonga ne da ci 6-3 6-7 (1-7) 7-6 (7-3) 6-4 a wasan da suka buga a yanayin da ya dara Celcius 30 a Paris.

Wawrinka mai shekaru 30 zai buga wasan karshe tsakanin Novak Djokovic ko kuma Andy Murray da rashin kyawun yanayi ya hana su fafatawa kamar yadda aka tsara.

Rabon da dan kasar Faransa ya dauki Roland Garros tun lokacin da Yannick Noah ya lashe gasar a shekarar 1983, yayin da Wawrinka ya dauki na farko a Australian a bara.