Barcelona ta lashe kofin zakarun Turai

Image caption 'Yan wasan Barca na murnar daukan kofi

Barcelona ta lashe kofin zakarun Turai karo na hudu bayan da ta doke Juventus 3-1 a karawar da suka yi ta karshe a kakar bana a Berlin.

Nasarar da Barca ta samu ya sa ta tashi da kofuna uku na wasanni daban daban a kasar wasannin bana.

Karawar da suka yi da Juventus ce wasa na karshe da Kyaftin din kulob din Xavi Hernandez ya buga wa Barca.

Xavi zai koma murza leda a Qatar bayan ya shafe shekaru 24 yana tare da Barcelona.

Ya buga wa kulob din wasanni 151, kuma shi ne dan wasan da yafi kowanne a kulob din yawan wasannin daya taka.