Ba ni da tabbacin zama a Barca —Enrique

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Luis Enrique ya buga wa Barcelona wasanni daga tsaakanin shekarar 1996 zuwa 2004

Kocin Barcelona Luis Enrique ya ki sanar da makomarsa a kungiyar: zai ci gaba da horar da ita a badi ko kuma a'a.

Enrique wanda ya maye gurbin Gerardo Martino, ya lashe kofuna uku da Barcelona a shekarar farko da ya fara jagorantar kungiyar.

Kocin ya fara daga kofin La Liga a bana a Barca daga nan ya lashe Copa del Rey, sannan ya dauki kofin Zakarun Turai bayan da suka doke Juventus da ci 3-1 a Berlin ranar Asbar.

Da aka tambaye shi ko zai ci gaba da jagorantar Barca a badi, sai ya amsa da cewar ba shi da masaniya, amma yana cike da farin ciki da yadda ya jagoranci kungiyar a bana.

Barcelona wacce ta buga wasanni 60, ta buga canjaras a karawa hudu sannan kuma aka doke ta a fafatawa shida a dukkan wasannin da ta buga a bana.