Aguero ya ci wa Argentina kwallaye uku

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sergio Aguero shi ne wanda ya fi yawan zura kwallaye a gasar Premier da aka kammala

Sergio Aguero ya zura kwallaye uku a raga a karon farko da yake buga wa Argentina wasanni a wasan sada zumunta da ta doke Bolivia da ci 5-0.

Argentina ta buga wasan ne a shirye-shiryen da take yi domin tunkarar Gasar cin Kofin Copa America da za a fara karawa ranar 11 ga wannan watan.

Dan wasan Manchester United Angel Di Maria ne ya fara ci wa Argentina kwallo a minti na 24 da fara tamaula.

Daga nan ne Aguero ya zura ta biyu a bugun fenariti, yayin da ya kara ta uku kuma ta biyu da ya ci, ya kuma kammala cin kwallonsa ta uku a karawar.

Yayin da ya rage 'yan mintuna a tashi daga wasan ne Di Maria ya kara ta biyar, kuma kwallo ta biyu da ya ci a wasan.

Kasar Chile ce za ta karbi bakuncin Gasar cin Kofin Copa Ameria, yayin da Argentina ke fatan daukar kofin, wanda rabonta da shi tun a shekarar 1993.

Argentina tana cikin rukunin da ya kunshi mai rike da kofin, Uruguay da Paraguay da kuma Jamaica.