Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Damben gargajiya da ake yi a Dakwa a Abuja

A ci gaba da wasan damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dakwa a Abuja, an dambata a wasanni da dama a ranar Lahadi.

An fara da dambe tsakanin Shagon Autan Faya daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa na tsawon turmi uku babu kisa.

Damben Sojan Kyallu daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu ya kayatar matuka, sai dai shi ma turmi uku suka yi babu kisa alkalin wasa Ali Kwarin Ganuwa ya raba wasan.

Sa zare da aka yi tsakanin Dogon Dan Digiri daga Kudu da Shagon Bahagon Musa sun yi gumurzu sun kuma fafata amma turmi biyu kawai suka yi.

Amma damben da aka fi biyan 'yan kallo shi ne tsakanin Shagon Alhazai daga Arewa da Shagon Kwarkwada daga Kudu.

Damben dai babu kisa amma yadda suka yi amarya suna dukan junansu ba tare da wani ya ja da baya ba, har sai da zare ya kwance shi ne abin da ya burge masoya wasan dambe.