U-20: Nigeria za ta kara da Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brazil ce ta jagoranci rukuni na biyar Nigeria ta yi ta biyu

Nigeria ta doke Hungary da ci 2-0 a Gasar cin Kofin matasa 'yan kasa da shekaru 20 da suka kara da sanyin safiyar Lahadi.

Wannan nasarar da Nigeria ta samu ta sa ta kai wasan kungiyoyi 16 da suka rage a gasar, wadanda za su buga wasannin gaba da ake yi a New Zealand.

Nigeria ta kammala wasanninta na rukuni na biyar da maki shida, wanda hakan ya sa za ta fafata da Jamus a wasan gaba.

Ita ma Hungary ta samu kai wa wasan gaba, yayin da aka zabota a matsayin cike gurbi, za kuma ta kara ne da Serbia.

Brazil ce ta jagoranci rukuni na biyar, sannan za ta buga wasan zagayen gaba ne da Uruguay a ranar Alhamis.