Nigeria da Sweden sun yi 3-3 a kwallon mata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria za ta buga wasan gaba da Australia ranar Juma'a

Nigeria da Sweden sun tashi wasa 3-3 a gasar cin kofin duniya ta mata da suka buga ranar Litinin a Canada.

Nigeria ce ta fara cin gida ta hannun Desire Oparanozie, sannan Nilla Fischer ta kara ta biyu a ragar saura minti 14 a ta fi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Nigeria ta farke kwallaye biyun da aka zura mata ta hannun Ngozi Okobi da kuma Asisat Oshoala.

Sweden ta kara kwallo ta uku ta hannun Linda Sembrandt, yayin da ya rage saura minti uku a tashi daga wasan Francisca Ordega ta farke kwallo ta ukun da aka ci Nigeria.

Nigeria wacce ta samu maki daya a wasa daya da ta yi, za ta buga wasan gaba da Australia ranar Juma'a, yayin da Sweden za ta fafata da Amurka ranar Asabar.