Rasha da Qatar sun bayar da na goro

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana zargin wasu jami'an Fifa da cin hanci da rashawa

Watakila Rasha da Qatar sun bayar da cin hanci ga jami'an Fifa wanda hakan ya sa aka ba su damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a kasashen su.

Tsohon mai bai wa Sepp Blatter shawara, Guido Tognoni, shi ne ya bayyana hakan ga BBC.

Tognoni ya ce a shekaru da dama da suka wuce, idan kana son cimma burinka, Fifa za ta iya karbar daloli daga hannunka.

Kafin wallafa wannan labarin, BBC ta tuntubi mahukuntan Fifa amma ba su ce komai ba kan lamarin.

Jami'an tsaron Switzerland suna bincike a kan hanyoyin da Fifa ta bi ta bayar da izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da ta 2022.

Tognoni, wanda ya yi aiki da Blatter daga shekarar 2001 zuwa 2003, ya ce da wuya a karbe tikitin karbar bakuncin gasar kofin duniya da aka bai wa Rasha da Qatar.