Alves ya sabunta kwantiragi a Barca

Hakkin mallakar hoto c
Image caption Dani Alves zai ci gaba da yin wasa a Nou Camp shekaru biyu masu zuwa

Dani Alves ya sabunta kwantiraginsa a Barcelona zuwa shekaru biyu masu zuwa, domin ya ci gaba da yi mata wasanni.

Dan kwallon Brazil wanda yarjejeniyarsa zai kare da Barca a karshen watannan, an yi ta rade radin zai koma taka leda a Liverpool ko kuma Manchester United a badi.

Alves wanda ya yi shekaru bakwai a Barca ya lashe kofin zakarun Turai uku da La Liga biyar da kuma kofin kalubalen Spaniya guda uku.

Fifa ta hana Barcelona musayar 'yan wasa, sakamakon karya kai'idar hukumar kan daukar 'yan wasa 'yan kasa da shekaru 18 da ta yi.

A ranar Litinin Barca ta dauki Aleix Vidal daga Sevilla wanda zai maye gurbin Alves a nan gaba, sai dai ba zai fara yi mata wasa ba har sai a Watan Janairun 2016.