Fifa: An dakatar da shirin gasar 2026

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin tafka cuwa-cuwa wajen sanar da gasar da za a yi a Qatar

An jinkirta shirin bayyana kasar da za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2026, saboda zarge-zargen da ya dabaibaye gasar da za a yi a shekara ta 2018 da kuma 2022.

Sakatare Janar na Fifa, Jerome Valcke ya ce babu tunani a soma batun kasar da za ta dauki bakuncin gasar a irin wannan lokacin.

A baya an shirya a kan cewa za a kada kuri'a a kan kasar da za ta dauki bakuncin gasar ta 2026 a wani biki da za a yi a Kuala Lumpur a watan Mayun 2017.

Amurka ce kan gaba wajen nuna sha'awar daukar bakuncin gasar, amma kuma Canada da Mexico da kuma Colombia sun nuna aniyarsu ta daukar bakuncin gasar.

Rasha da Qatar ne za su dauki bakuncin gasar a 2018 da kuma 2022 bayan da aka sanar da nasararsu a wani zabe da manyan jami'an Fifa suka yi a watan Disambar 2010.