Newcastle ya sallami John Carver

Image caption Wasanni uku Carver ya ci daga wasanni 20 da ya jagoranci Newcastle United

Kulob din Newcastle United ya raba gari da kocin rikon kwarya John Carver da mataimakinsa Steve Stone.

Carver mai shekaru 50, ya jagoranci kulob din wasannin 20, a inda ya lashe wasanni uku kacal, bayan da ya maye gurbin Alan Pardew wanda ya koma Crystal Palace.

Da kyar da gumin goshi Newcastle ya samu tikitin ci gaba da buga gasar Premier badi a wasan karshe na gasar bana.

Ana hasashen cewa tsohon kociyan tawagar kwallon kafar Ingila Steve McClaren wanda ya taba horar da Derby ne zai maye gurbin Carver a Newcastle.