West Ham ta nada sabon koci Bilic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Slaven Bilic ya buga wa West Ham United wasanni

West Ham United ta dauki tsohon dan wasanta mai tsaron baya Slaven Bilic a matsayin sabon kociyanta.

Bilic mai shekaru 46, ya maye gurbin Sam Allardyce wanda ya ajiye aikin, bayan da ya jagoranci kungiyar shekaru hudu.

Kocin ya rattaba kwantiragin shekaru uku da West Ham wacce ta kammala Premier bana a mataki na 12.

Ya buga wasa a Upton Park a shekarar 1996 zuwa 1997, ya kuma horar da tawagar kwallon kafar Croatia shekaru shida.

Haka kuma ya horar da Lokomotiv Moscow da kuma Besiktas wacce ya ajiye aikin a watan Mayu.