Za mu kare bayan Man United —Smalling

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester United ta kammala gasar Premier a mataki na hudu a kan teburi

Chris Smalling ya ce da shi da Phil Jones sun dace wajen aikin tsare bayan kulob din Manchester United a wasannin da take yi.

Bayan da Rio Ferdinand da Nemanja Vidic suka bar United a bara, kulob din ya saka 'yan wasan biyu sun maye gurbinsu a bana a wasannin da ya yi.

Louis van Gaal ne ya yanke wannan shawarar a inda United ta kare a mataki na hudu a teburin Premier, kuma ita ce ta hudu a gasar Premier da ba'a zura mata kwallaye da dama ba.

Smalling dan kwallon Ingila ya ce "A shirye muke mu cike gurbin da United ta yi rashi a baya".

Duk da 'yan wasan biyu suna tsaron baya daga tsakiya a United, ba wannan salon suke yi wa Ingila tamaula ba.

Manchester United za ta buga wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta kakar wasannin 2015-16.