Messi zai gurfana kan kin biyan haraji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekaru baya da suka wuce Messi da mahaifinsa sun biya mahukuntan Spaniya euro miliyan biyar

Dan kwallon Argentina da Barcelona, Lionel Messi, na daf da gurfana a gaban kotun Spaniya wacce taki amincewa da daukaka karar da ya yi kan kin biyan haraji da ake zarginsa.

An zargi Messi da mahaifinsa Jorge da zambar kin biyan haraji ga mahukuntan Spaniya da ya kai euro miliyan hudu.

Kotun ta yanke hukuncin cewa ba za a bai wa Messi kariyar cewa bai san yadda a ke gudanar da harkokin kudadensa ba.

Dukkanninsu biyu sun musanta zargin da ake yi musa na kin biyan haraji daga shekarar 2007 zuwa 2009.

Messi da mahaifinsa sun biya kudi da suka kai euro miliyan biyar ga hukuma, kwatankwacin kudaden da ake zargin su da kin biya a watan Agustan 2013.

Messi ya koma taka leda a Barcelona yana da shekaru 13 a shekarar 2000, kuma shekaru uku tsakani ya fara buga mata wasanni.