Marta ta kafa tarihin yawan cin kwallaye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Marta ta halarci gasar kofin duniya karo biyar a jere

'Yar wasan tawagar kwallon kafar Brazil Marta, ta kafa tarihin wacce ta fi yawan cin kwallaye a gasar cin kofin duniya ta mata.

Marta ta ci kwallo a wasan da Brazil ta doke Korea ta Kudu da ci 2-0 a gasar cin kofin duniya ta mata da ake yi a Canada, kuma kwallo ta 15 kenan da ta ci a tarihin gasar.

Mai shekaru 29, ta zura kwallon ne a bugun fenariti wanda hakan ya sa ta dara Birgit Prinz ta Jamus a yawan cin kwallaye a wasannin cin kofin duniya ta mata.

Marta wacce ta fara buga wa Brazil wasa shekaru 12 da suka wuce, ta ci kwallaye 92 daga cikin wasanni 93 da ta yi wa kasarta.

Formiga ce ta fara ciwa Brazil kwallon farko wacce ita ma ta kafa tarihin 'yar wasa mai yawan shekaru da ta zura kwallo a gasar tana da shekaru 37.

Brazil ce ta jagoranci rukuni na biyar a wasannin, bayan da Spaniya da Costa Rica suka tashi wasa kunnen doki a ranar Talata.