Blatter zai bar Fifa 16 ga Disamba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blatter zai ajiye aiki bayan shekaru 17 da ya yi yana shugabantar fifa

Sepp Blatter zai iya barin shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa ranar 16 ga watan Disamba.

BBC ta fahimci cewar watakila a ranar ce kuma za a yi taron gaggawa a hukumar a Zurich domin zaben cike gurbin.

A ranar ce ake sa ran mambobin hukumar 209 za su halarci Switzerland domin zaben sabon shugaban Fifa.

Blatter mai shekaru 79 ya yi murabus daga shugabancin Fifa kwanaki hudu da sake zabarsa domin ya jagoranci hukumar karo na biyar.

Shugaban ya amince ya yi ritaya ne bisa zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye hukumar.

An damke wasu jami'an Fifa bakwai ranar 27 ga watan Mayu a Zurich a wani mamaye da jami'an tsaro suka kai a otal din da suka sauka.

Mutanen suna daga cikin jami'an Fifa 14 da Amurka ke zargi da cin hanci da rashawa da halasta kudaden haram.