Fifa: An kori Walter bisa barkwanci da ya yi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana tuhumar Walter da zargin cin hanci da rashawa a hukumar Fifa

An sallami Daraktan harkokin sadarwa na FIFA Mr Walter de Gregorio,wanda ya kasance na baya bayan nan da ake tuhuma kan zargin badakalar cin hancin da ta dabaibaye hukumar.

BBC ta gano cewa shugaban hukumar Sepp Blatter ya umarci Mr de Gregorio ya yi murabus daga mukaminsa, bayan da wata mujalla ta yi masa kakkausar suka kan shafawa FIFA bakin fenti.

Wani barkwanci da Mr de Gregorio yayi a gidan Talabijin na Switzerland dake danganta cafkewar da yansanda suka yiwa wasu shugabannin hukumar ta FIFA ne ake ganin me yiwuwa shi ne ya sa ba a bankado shi ba.

A makon da ya gabata ne Mr Sepp Blatter ya sanar da cewa zai sauka daga mukaminsa na shugaban hukumar.

Mr de Gregorio zai cigaba da kasancewa mai bada shawara har ya zuwa karshen wannan shekarar.