Manyan 'yan wasa na son koma wa City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption City ta kasa taka rawar gani a gasar zakarun Turai

Shugaban Manchester City, Khaldoon Al Mubarak ya ce manyan 'yan wasa na son koma wa kulob din ba wai domin kudi ba.

Babban dan kasuwar daga gabas ta tsakiya ya ce dole ne City ke biyan makudan kudade domin manyan 'yan wasa su koma kungiyar tun daga lokacin da ya sayi kulob din a shekara ta 2008.

'Yan wasa na farko da suka siyo su ne 'yan Brazil Robinho a kan fan miliyan 32.5 da kuma Jo a kan fan miliyan 19.

Daga wasu daga cikin manyan 'yan wasan da City ta siyo a 2008 zuwa 2009:

  • Robinho daga Real Madrid a kan fan miliyan 32
  • Jo daga CSKA Moscow a kan fan miliyan 19
  • Nigel De Jong daga Hamburg a kan fan miliyan 18
  • Craig Bellamy daga West Ham a kan fan miliyan 14
  • Wayne Bridge daga Chelsea a kan fan miliyan 12
  • Shaun Wright-Phillips daga Chelsea a kan fan miliyan 10
  • Pablo Zabaleta daga Espanyol a kan fan miliyan 6.45
  • Vincent Kompany daga Hamburg a kan fan miliyan 6
  • Shay Given daga Newcastle a kan fan miliyan 5