'Fitattun 'yan wasa na kwadayin City'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City ta kammala a mataki na biyu a teburin Premier bana

Shugaban Manchester City, Khaldoon Al Mubarak, ya yi amanna cewa fitattun 'yan wasan kwallon kafa na kwadayin buga leda a kulob din ba domin albashi mai tsoka ba.

Khaldoon ya ce tun lokacin da suka sayi City a shekarar 2008 suka rinka biyan albashi mai tsoka ga 'yan wasa domin jan hankalin kwararrun 'yan wasa da su dawo City buga kwallo.

'Yan wasan farko-farko da kulob din ya fara saya sun hada da Robinho kan kudi sama da fan miliyan 32 da kuma Jo, wanda aka sayo kan kudi fan miliyan 19.

Al Mubarak ya ce "Mun zama kulob din da manyan 'yan wasa ke son su buga wa tamaula, muna biyan albashi mai tsoka domin jawo hankalin fitattun 'yan kwallo".

Al Mubarak ya ce City tana da kayayyaki da tanade-tande da za ta iya daukar duk wani sanannen dan wasa a duniya, amma za ta fuskanci kalubale da zarar an bude kasuwar musayar 'yan kwallo ranar 1 ga watan Yuli.