U-20: Jamus ta fitar da Nigeria

Image caption Nigeria ba ta taba lashe kofin matasa 'yan kasa da shekaru 20 ba

Nigeria ta fice daga gasar cin kofin matasa ta duniya 'yan kasa da shekaru 20, bayan da Jamus ta doke ta da ci daya mai ban haushi.

Jamus ta zura kwallonta ne ta hannun Levin Oztunali a minti na 19 da fara wasa, wanda hakan ya sa ta kai wasan daf da na kusa da karshe.

Nigeria dai ba ta taba lashe kofin matasa 'yan kasa da shekaru biyu ba, illa dai ta ba yin ta biyu a gasar a shekarar 1989 da kuma 2005.

Jamus za ta kara da Mali a wasan daf da na karshe ranar Lahadi, yayin da Senegal za ta fafata da Uzbekistan a Wellington.