Ingila ta doke Slovenia da ci 3-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ta yi shekara daya ba'a doke ta a wasan kwallon kafa ba

Tawagar kwallon kafar Ingila ta samu nasara a kan Sloveniya da ci 3-2 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da suka kara ranar Lahadi.

Novakovic ne ya fara ci wa Slovenia kwallo daga baya Wilshere ya farke wa Ingila kwallon da aka zura mata.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Wilshere ya ci wa Ingila kwallo ta biyu kuma Pecnik ya farke wa Slovenia, minti biyu tsakani Rooney ya ci kwallo ta uku a raga.

Da wannan nasarar da Ingila ta samu ya sa ta lashe dukkan wasanni shida da ta yi a rukuni na biyar, kuma ita ce jagaba a kan teburi.

Haka kuma ta yi shekara daya ba'a doke ta a wasan tamaula ba, tun bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Italiya a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a shekarar 2014.