Nadal ya lashe kofin Mercedes a Stuttgart

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Nadal ya koma mataki na 10 a jerin 'yan kwallon tennis da suka fi iya wasan a duniya a farkon watannan

Rafael Nadal ya lashe kofin Mercedes a Stuttgart, bayan da ya doke Viktor Troicki karo na farko da ya yi wasan a kan ciyawa tun a shekarar 2010.

Nadal dan kasar Spaniya wanda Novak Djokovic ya doke shi a gasar French Open ya doke Troiki da ci 7-6 (7-3) 6-3.

Nasarar da Nadal ya samu za ta kara daga martabarsa a jerin 'yan wasan tennis da suka fi yin fice a duniya, bayan da ya fada mataki na 10 a farkon watannan.

Nadal zai kara da Alexandr Dolgopolov dan kasar Ukraine a wasan kwallon tennis da zai yi na gaba, kafin a fara gasar Wimbledon a ranar 29 ga watan Yuni.