An gargadi Blatter kar ya sake shawara

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Sepp Blatter ya yi shekaru 17 yana jagorancin hukumar Fifa

Shugaban sashen binciken kudi da tabbatar da cewa an kashe su bisa ka'ida na Fifa, Domenico Scala, ya gargadi Sepp Blatter da kada ya sauya aniyarsa ta yin murabus daga hukumar.

Scala ya yi wannan gargadin ne bayan da wadansu rahotanni ke cewa Blatter zai ci gaba da jagorancin hukumar, duk da sanarwar da ya fitar cewar zai sauka daga shugabancin hukumar a baya.

Jami'in ya bayar da shawarar cewa shugaba da mukarrabansa su rika yin shekaru 12 bisa kan mulki.

Blatter, mai shekaru 17, ya ce zai yi murabus daga shugabancin Fifa sakamakon zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka dabaibaye hukumar.

A watan Disamba ake sa ran Fifa za ta gudanar da babban taronta a Zurich domin zaben wanda zai maye gurbin Sepp Blatter.