Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Shagon Musan Kaduna daga Arewa ne ya kashe Audu na Mai Kashi a wannan takawar

An ci gaba da yin wasannin damben gargajiya da ake fafatawa a gidan damben Ali Zuma na Bala Shagari na Altine Kajiji dake Dakwa a Abuja da aka kara ranar Asabar.

An fara yin wasa ne tsakanin Shagon Inda daga Arewa da Garkuwan Shagon Mada daga Kudu, a inda suka buga turmi uku sai dai babu kisa a damben.

Sai dai damben da aka yi tsakanin Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Shagon Audu na Mai Kashi daga Kudu ya kayatar inda suka dambata tsawon turmi uku.

Bayan da suka shiga turmi na uku ne Shagon Musan Kaduna ya kashe Shagon Audu na Mai Kashi kuma sai da ya fadi kasa wanwar.

Daga karshe an saka zare tsakanin Bahagon Alin Tarara daga Arewa da Bahagon Sisco na tsawon turmi uku, sai dai babu kisa alkalin wasa Alin Kwarin Ganuwa ya raba wasan.