Valdes zai maye gurbin De Gea a United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Valdes shohon golan Barca ya kamawa United wasanni biyu a bana

A shirye Victor Valdes yake ya maye gurbin David De Gea da zarar ya bar Manchester United in ji Edwin van der Sar.

De Gea, mai shekaru 24 wanda saura shekara daya ya rage kwantiraginsa ya kare a United ana rade-radin zai koma taka leda Real Madrid ne a badi.

Van der Sar ya shaidawa BBC cewar watakila tuni United ta yanke shawarar wanda zai maye gurbin De Gea da zarar ya bar kulob din.

Valdes ya yi atisaye da United lokacin da ya warke daga raunin da ya ji sannan ta dauke shi kwantiragin shekara daya a watan Janairu, ya kuma yi mata wasanni biyu a kakar wasan bana

De Gea wanda United ta sayo kan kudi sama da fam miliyan 18, shi ne ya maye gurbin Van der Sar wanda ya yi ritaya daga taka leda a shekarar 2011