Adebayor ba shi da tabbas a Togo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Adebayor wanda ke taka leda a Tottenham dake buga gasar Premier

Emmanuel Adebayor ba shi da tabbas a tawagar kwallon kafar Togo bayan da aka karbe kambun kyaftin a karawar da suka yi da Liberia.

Sai a ranar da za su kara da Liberia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2017 aka sanar masa cewa ba shi ne kyaftin a wasan ba.

Adebayor mai shekaru 31 shi ne ya zura kwallo a wasan da suka doke Liberia da ci daya mai ban haushi a Togo.

Sai dai dan wasan ya ce ba shi da tabbaci idan zai buga karawa ta biyu da za su yi a Djibouti a watan Satumba.

Dan kwallon ya ce ya rike kyaftin din tawagar Togo shekaru kusan takwas, amma dare daya an ce ba shi ne ba, watakila ya yi zaman benci a wasa na biyu.