Damben gargajiya da ake yi a Abuja

Image caption Damben Alin Tarara da Sisco babu kisa a wannan takawar da suka yi

An ci gaba da karawa a wasannin damben gargajiya da ake yi a gidan Ali Zuma dake Dakwa a Abuja Nigeria ranar Lahadi.

An fara da dambe ne tsakanin Shagon Habu Nasarawa daga Arewa da Dan Digiri daga Kudu na tsawon turmi uku babu kisa aka raba wasan.

An kuma sa zare tsakanin Shagon Dan'abata Mai daga Kudu da Bahagon Shagon Nabacirawa daga Arewa.

Damben ya kayatar sai dai babu kisa a turmi uku da suka fafata, a inda alkalin wasa Alin Kwarin Ganuwa ya raba karawar.

Wasa na karshe da aka yi tsakanin Bahagon Sisco daga Arewa da Bahagon Alin Tarara daga Arewa ya kayatar matuka.

Sai dai shi ma wasan turmi uku da suka yi babu kisa aka raba raba damben ganin dare ya riga ya kawo.