AC Milan ta nada Mihajlovic kociyanta

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption AC MIlan ta gaza samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai da za a yi a badi

Kungiyar AC Milan ta Italiya ta dauki Sinisa Mihajlovic a matsayin sabon kocinta bayan ta kori Filippo Inzaghi.

Mihajlovic tsohon dan wasan Yugoslavia kuma mai tsaron baya mai shekaru 46 ya rattaba kwantiragin shekaru biyu, bayan da ya bar Sampdoria.

Inzaghi, wanda ya yi wa Milan wasa daga shekarar 2001 har lokacin da ya yi ritaya a shekarar 2012, ya maye gurbin Clarence Seedorf a watan Yunin bara.

Milan ta kammala gasar Serie A na bana a mataki na 10 da maki 35, bayan da Juventus ta lashe kofin gasar bana.

Mihajlovic ya buga wa Roma da Sampdoria da Lazio da kuma Inter Milan wasanni a shekaru 20 da ya yi a matsayin kwararren dan kwallo.

Bayan da ya yi ritaya daga buga tamaula ya yi mataimakin koci a Inter, sannan ya jagoranci Bologna da Cataniya da kuma Fiorentina

Kocin ya kuma horar da tawagar kwallon kafar Serbia a watan Afirilun 2012, a inda ya ci wasanni bakwai sannan ya yi rashin nasara a karawa takwas.