Blazer ya yi leken asiri a hukumar Fifa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chuck yana daga cikin jami'an Fifa da ya tabbatar da ana cin hanci da rashawa a hukumar

Tsohon babban jami'in Fifa ya yi aikin leken asiri na tsahon watanni 18 tare da masu bincike a lokacin da yake yin aiki da hukumar.

Chuck Blazer, mai shekaru 70, ya kulla yarjejeniyar taimakawa masu shigar da kara 'yan Amurka, bayan da aka tuhume shi da zargin cin hanci da rashawa.

An fitar da kunshin yarjejeniyar da suka kulla bayan da alkalin wata kotu ya amince da a nuna wa wasu kafafen yada labarai biyar shirin da suka yi.

Takardun da aka fitar sun nuna Blazer ya fara bayar da hadin kai tun daga watan Disambar 2011.

Blazer dan kasar Amurka ya yi aiki a matsayin mamba a kwamitin amintatu na Fifa daga tsakanin 1997 zuwa 2013.

A watan jiya ne aka damke wasu jami'an Fifa 14 kan zargin cin hanci da rashawa da suka tafka tsawon shekaru 24 a hukumar.