Dan Madrid na son buga wa Nigeria kwallo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mahaifin Derik Osede Prieto dan Nigeria ne

Matashin dan kwallon Spain, Derik Osede Prieto ya shaidawa BBC cewar yanason ya buga wa Nigeria kwallo.

Dan wasan bayan mai shekaru 22, wanda ake kira Derik a takaice, ya bugawa Spain tamaula har sau biyu a matakin 'yan kasa da shekaru 21.

Derik wanda ke buga wa karamar tawagar Real Madrid na da damar bugawa Super Eagles kwallo saboda mahaifinsa dan Nigeria ne.

Dokar Fifa ta ba da dama ga dan kwallo ya canza kasar da ya ke bugawa kwallo idan har bai buga wa babbar tawagar wata kasa ba.

"Tsawon rayuwata a Spain na taso, amma ina son wata dama ta zo min domin ya hade da kakannina daga Nigeria," in ji Derik.