'Falcao da Cuadrado za su haskaka a Chelsea'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Falcao ya buga wa Manchester United wasanni aro a bana

Kociyan tawagar kwallon kafar Colombia, Jose Pekerman, Radamel Falcao da Juan Cuadrado za su taka rawar gani a kulob din Chelsea a badi.

Chelsea na dab da dauko Radamel Falcao daga Monaco domin ya buga mata tamaula aro a badin.

Falcao -- mai shekaru 29 wanda yake buga wa Colombia gasar Copa America a Chile -- ya ci wa Manchester kwallaye hudu daga wasanni 29 da ya buga mata wasa aro a bana.

Chelsea ta dauko Cuadrado daga Fiorentina a kan kudi sama da £23m a watan Fabrairu, amma bai buga mata wasanni da dama ba.

Pekerman ya ce 'yan wasan biyu za su taimakawa junansu buga gasar Premier, sannan su kara samun kwarewar da za ta taimakawa Colombia a wasanninta.