Za a ci gaba da wasannin Premier a Nigeria

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Giwa FC ce ke mataki na daya a kan teburin Premier

Enyimba International za ta karbi bakuncin Heartland a ci gaba da gasar Premier wasannin mako na 12 ranar Laraba a garin Aba.

Ita ma Lobi Stars za ta karbi bakuncin Nasarawa United, a inda Akwa United da Kwara United za su kece raini da kuma gumurzu tsakanin Rangers da Abia Warriors.

Sauran wasannin da za a yi Sharks za ta karbi bakuncin El-Kanemi, yayin da Shoting Stars za ta ziyarci Bayelsa United, sai karawa tsakanin Ifeanyiubah da Dolphins.

Kano Pillars, mai rike da kofin Premier, za ta karbi bakuncin Giwa FC wacce take mataki na daya a kan teburi a ranar Alhamis a filin wasa na Sani Abacha.

Ga wasannin mako na 12 da za a buga:

  • Ifeanyi Uba - Dolphins FC
  • Sharks FC - El-Kanemi Warriors
  • Taraba FC - Wikki Tourists
  • Enyimba Aba - Heartland FC
  • Bayelsa United - Shooting Stars FC
  • Lobi Stars - Nasarawa United FC
  • Akwa United - Kwara United
  • Enugu Rangers Enugu Rangers
  • Sunshine Stars Sunshine Stars