Enyimba ta samu maki uku a kan Heartland

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin mako na 12 a gasar Premier Nigeria

Enyimba International ta doke Heartland da ci 2-0 a gasar Premier wasannin mako na 12 da suka yi a Aba ranar Laraba.

Chinonso Okonkwo ne ya fara ci wa Enyimba kwallo a raga saura minti biyar a ta fi hutu, kuma bayan da aka dawo daga hutu ne Christian Obiozor ya kara cin kwallo ta biyu.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Sharks da El-Kanemi sun tashi canjaras, haka ma karawa tsakanin Bayelsa United da Shooting Stars suka tashi wasan babu ci.

Lobi Stars kuwa ta samu nasara a kan Nasarawa United da ci 2-1, yayin da FC Ifeanyiubah ta doke Dolphins da ci daya mai ban haushi.

Ga sakamakon wasannin da aka yi:

  • FC Ifeanyiubah 1-0 Dolphins
  • Sharks 0-0 El-Kanemi Warriors
  • Enyimba 2-0 Heartland
  • Bayelsa United 0-0 Shooting Stars
  • Lobi Stars 2-1 Nasarawa United
  • Akwa United 2-1 Kwara United
  • Rangers 1-0 Abia Warriors