Musa Bility zai yi takarar kujerar Fifa

Image caption Musa Bility shi ne mutun na biyu da ya sanar da zai yi takarar kujerar Fifa

Shugaban hukumar kwallon kafar Liberia Musa Bility ya sanar da cewar yana shirin zai tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa.

Bility mai shekaru 48, ya ce wa'adin nahiyar Afirka ne ta shugabanci Fifa, kuma shi ne mutun na biyu da zai yi zawarcin kujerar bayan Zico na Brazil.

Shugaban hukumar kwallon kafa na Afirka Issa Hayatou shi ne mutumin farko a Afirka da ya taba yin takarar kujerar Fifa.

Hayatou ya sha kaye a hannun Sepp Blatter a zaben hukumar da aka gudanar a shekarar 2002.

Ranar 2 ga watan Yuni Blatter ya sanar da cewar zai sauka daga shugabancin Fifa, bayan da zargin cin hanci da Rashawa ya mamaye hukumar.