Norwich za ta dauki Youssouf Mulumbu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Norwich ta samu gurbin buga gasar Premier badi

Kungiyar Norwich City wacce ta samu gurbin buga gasar Premier badi, za ta dauko tsohon dan kwallon West Bromwich Albion Youssouf Mulumbu.

Mulumbu, mai shekaru 28, dan kasar Jamhuriyar Congo, kwantiraginsa ce ta kare da Baggies a bana.

Dan kwallon ya buga wasanni 211 a Albion tun lokacin da ya koma kungiyar daga Paris St-Germain a shekarar 2009.

Shi ma takwaransa Graham Dorrans zai bar taka leda a The Hawthorns domin ya koma Norwich City.

Norwich na daf da sanar da shirin da take yi na dauko Mulumbu ga magoya bayanta da 'yan jaridu.