Ashley ya yi wa Ayew maraba a Swansea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ayew zai fara buga gasar Premier a badi da Swansea

Kyaftin din Swansea City, Ashley Williams, ya ce dauko dan kwallon Ghana, Andre Ayew, ya nuna kyakkawar aniyar da kulob din ke da shi a badi.

Ayew, mai shekaru 25, zakaran kyautar dan wasan Afirka da BBC ta karrama a shekarar 2011, ya buga wa tawagar kwallon kafar Ghana wasanni 62, ya kuma ci kwallaye 11.

Dan wasan ya sanya hannun a kan kwantiragin shekaru hudu a Swansea, bayan da yarjejeniyarsa ta kare da Marseill a bana.

Williams ya ce "Kulob din yana kan turbar ci gaba domin ya yi babban kamu da ya dauko Ayew".

Bafetimbi Gomis ne ya raga wanda ke ci wa kulob din kwallaye, bayan da Nelson Oliveira ya koma Benfica, sannan aka sayar da Wilfred Bony ga Manchester City.

Swansea City za ta fara wasan Premier badi da Chelsea a Stamford Bridge, sannan ta kammala a gida da Manchester City ranar 15 ga watan Mayun badin.