Tennis: Murry ya lashe kofin Queens

Image caption Kofi na hudu kenan da ya lashe a gasar Queen

Andy Murray ya lashe gasar Queens da aka kammala a Landan, bayan da ya doke Kevin Anderson a ranar Lahadi.

Murray ya doke Kevin Anderson ne da ci 6-3 6-4 a mintuna 64 da suka yi suna fafatawa a Aegon dake Landan.

Wannan ne karo na hudu da dan wasan ya lashe kofin, bayan da ya dauka a shekarar 2009 da 2011 da kuma 2013.

Haka kuma Murray yabi sahun John McEnroe da kuma Boris Becker wadanda kowannensu ya lashe kofin sau hudu.