Messi ya buga wa Argentina wasanni 100

Image caption Messi ya fara buga wa babbar tawagar kwallon kafar Argentina tamaula a shekarar 2005

Lionel Messi ya buga wa tawagar kwallon kafar Argentina wasa na 100 a karawar da suka doke Jamaica a gasar Copa America da ake yi a Chile.

Argentina ta samu nasara ne a fafatawar da ci daya mai ban haushi, yayin da Gonzalo Higuain ne ya ci kwallon a minti na 11 da fara tamaula.

Messi wanda ya fara buga wa babbar tawagar kwallon kafar Argentina tamaula a shekarar 2005 ya buga mata wasanni 100 ya kuma zura kwallaye 46 a raga.

Da wannan nasarar da Argentina ta samu ya sa ta zagoranci rukuni na biyu, za kuma ta buga wasan zagayen gaba na kungiyoyi 16 da za su rage a gasar.

Uruguay da Paraguay sun kai zagayen gaba daga rukuni na biyun, bayan da suka buga 1-1 a wasan da suka yi gumurzu.

Paraguay ce ta yi na biyu a rukunin biye da Argentina, yayin da aka zabo Uruguay a matsayin cike gurbi, bisa rawar da ta taka a wasannin.