NFF za ta binciki Stephen Keshi

Image caption Wannan ne karo na uku da Keshi ke horar da tawagar Super Eagles

Hukumar kwallon kafar Nigeria NFF za ta binciki Stephen Keshi, kan wani rahoto da ya ce kocin ya mika takardun neman izinin horar da tawagar kwallon kafar Ivory Coast.

A ranar Juma'a ne hukumar kwallon kafar Ivory Coast ta ce ta karbi takardun masu horar da kwallon kafa 59 da suke zawarcin koyar da tawagar kwallon kafar kasa.

Hukumar ta kuma fitar da jerin sunayen masu son horar da kasar tamaula su 58 ciki har da sunan Keshi a ciki.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta ce za ta kafa kwamitin bincike domin tabbatar da idan Keshi ya yi zawarcin aikin horar da kasar Ivory Coast.

NFF ta kulla yarjejeniyar shekaru biyu da Keshi a watan Afirilun da ya wuce, kuma karo na uku kenan da yake jagorantar Super Eagles.