Rangers ta doke Warri Wolves da ci 1-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption sakamakon gasar Premier Nigeria wasannin mako na 13

Kungiyar Enugu Rangers ta doke Warri Wolves da ci daya mai ban haushi a gasar Premier Nigeria wasan mako na 13 da suka kara a Warri ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin Sunshine Stars ta ci gaba da rike matsayinta na daya a kan teburi bayan da ta doke Kano Pillars da ci 3-0 a Akure.

El-Kanemi kuwa ba ta ji da dadi ba a hannun Ifeanyiubah, bayan da aka casa ta 4-1 a Katsina sabon gidan da ta koma yin wasanni.

Ita kuwa Giwa FC ta tashi wasa kunnen doki da Dolhins a Port Harcourt, yayin da fafatawa tsakanin Lobi Stars da Kwara shi ma suka tashi 1-1.

Ga sakamakon wasannin mako na 13 da aka buga:

  • Abia Warriors 1-0 Akwa United
  • Dolphins 1-1 Giwa FC
  • El-Kanemi Warriors 1-4 FC Ifenyiuba
  • Wikki Tourists 3-0 Sharks
  • Heartland 2-0 FC Taraba
  • Shooting Stars 0-0 Enyimba
  • Nasarawa United 1-0 Bayelsa
  • Kwara United 1-1 Lobi Stars
  • Warri Wolves 0-1 Rangers
  • Sunshine Stars 3-0 Kano Pillars