Wikki Tourists za ta karbi bakuncin Sharks

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption za a ci gaba da wasannin mako na 13 a gasar Premier Nigeria

Wikki Tourists ta Bauchi za ta kara da Sharks ta Port Harcourt a gasar Premier Nigeria wasannin mako 13 ranar Lahadi.

Sauran wasannin da za a yi Enyimba za ta ziyarci Shooting Stars, yayin da Kwara United za ta kara da Lobi Stars da kuma fafatawa tsakanin Heartland da Taraba United.

Wasan da zai ja hankalin masu bibiyar gasar Premier Nigeria shi ne tsakanin Sunshine Stars wacce ke mataki na daya a kan teburi da Kano Pillars mai rike da kofin bara.

Bayan da aka buga wasan mako na 12 Sunshine Stars ce ke matsayi na daya a kan teburi da maki 23, yayin da Enyimba ke mataki na biyu da maki 22 sai Kano Pillars da maki 21 a matsayi na uku.

Ga wasannin mako na 13 da za a buga:

  • Dolphins vs Giwa FC
  • El-Kanemi Warriors vs FC Ifeanyiubah
  • Wikki Tourists vs Sharks
  • Heartland vs FC Taraba
  • Shooting Stars vs Enyimba
  • Nasarawa United vs Bayelsa United
  • Kwara United vs Lobi Stars
  • Warri Wolves vs Rangers
  • Sunshine Stars vs Kano Pillars
  • Abia Warriors vs Akwa United