Neymar ya gama buga Copa America

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Brazil ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar Copa America a Chile

Neymar ba zai ci gaba da buga gasar Copa America da Chile ke karbar bakunci ba, bayan da Brazil ta ki daukaka kara kan dakatar da shi daga buga wasanni hudu da aka yi.

An bai wa Neymar jan kati ne a lokacin da aka tashi wasan da Brazil ta doke Colombia da ci daya mai haushi a makon jiya.

Tun a baya kocin Brazil Dunga ya ce hukumar kwallon kafar kasar za ta daukaka kara kan hukuncin da aka yankewa dan kwallon.

Neymar zai bar sansanin tawagar kwallon kafar Brazil ranar Litinin, bayan da hukumar kwallon kafar kasar ta sanar da cewar ba za ta daukaka kara ba.

Dan kwallon bai buga karawar da Brazil ta doke Venezuela da ci 2-1 a ranar Lahadi ba, nasarar da yasa za ta fafata da Paraguay a ranar Asabar a wasan daf da na kusa da karshe.