Traore zai fara buga wa Chelsea tamaula

Hakkin mallakar hoto
Image caption Chelsea ce ta dauki Premier bana da aka kammala

Dan kwallon tawagar Burkina Faso, Bertrand Traore, zai fara buga wa Chelsea tamaula, bayan da ya samu takardar izinin taka leda a Burtaniya.

Traore, mai shekaru 19 ya saka hannu kan yarjejeniya da Chelsea a watan Janairun 2014, amma rashin takardar izini zuwa can buga tamaula ya hana shi komawa Stamford Bridge.

Hakan ne ma yasa Chelsea ta baya da shi aro ga kulob din Vitesse Arnhem dake Netherlands.

Bayan da aka kammala gasar wasannin bana ne the Blue ta kara neman izini ga mahukunta, wadanda suka amince Traore ya fara buga wa Chelsea tamaula a badi.

Chelsea za ta buga atisayen tunkarar wasannin badi da New York Red Bulls da Paris St-Germain da kuma Barcelona a Amurka.