An kama Pulvirenti a kan cinikin wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasanni biyar zuwa shida aka yi ciniki ciki har da bai wa 'yan wasa kudade

Jami'an tsaro sun kama shugaban Catania, Antonino Pulvirenti, daya daga cikin mutane bakwai da ake zargi da hannu a cinikin wasannin kwallon kafar gasar Seria B na Italiya.

Cikin wadanda aka kama har da mataimakin Pulvirenti, Pablo Cosentino da kuma tsohon daraktan wasanni Daniele Delli Carri.

'Yan sandan Catania sun kama mutanen ne bisa zargin cin hanci da cinikin gasar wasanni a Italiya.

Sai dai jami'an ba su fitar da bayanan jerin wasannin da ake zargin su da sayar wa ba.

Mai shigar da kara Giovanni Salvi ya ce a kalla wasanni biyar zuwa shida ne aka sayar ko aka shirya, har ma aka bai wa wasu 'yan wasa kudade.